Najeriya za ta kara da Equatorial Guinea a wasan farko a rukuni na daya ranar Lahadi a Abidjan a gasar kofin Afirka da ake yi a Ivory Coast.
Ga jerin wasu abinda ya kamata ku sani kan wasan:
Najeriya
Wannan shi ne karon farko da za a kara tsakanin Najeriya da Equatorial Guinea a gasar kofin Afirka.
Amma sun kara a wasan neman shiga gasar kofin duniya a 2010, inda Super Eagles ta yi nasarar cin (1-0; 2-0).
Wannan shi ne karo na 20 da Najeriya za ta kara a Afcon, bayan da ta dauki uku, wato a 1980 da 1994 da kuma 2013 da kai wa wasan karshe sau 14 baya daga gasa 17.
Super Eagles ta yi rashin nasara a wasan karshe a 1984 da Ivory Coast ta dauki nauyi ta kuma lashe kofin, bayan cin 3-1.
Nijeriya ta yi nasara 12 daga wasa 15 baya da rashin nasara uku, rabonda ta buga canjaras tun 2013 tsakaninta da Zambia da suka tashi 1-1.
Super Eagles ta zura kwallo 22 a wasa shida a cikin rukuni a neman shiga Afcon 2023, itace kan gaba a yawan zura kwallaye tsakanin tawaga 24 da za ta kara a gasar bana.
Equatorial Guinea
Wannan shi ne karo na hudu da Equatorial Guinea za ta buga gasar ta AFCON, bayan da ta karbi bakuncin biyu daga ciki.
Tawagar ta taba kai wa matakin quarter-finalists a 2012 da kuma 2020 ta kuma kare a mataki na hudu a 2015.
Equatorial Guinea ba ta taba zura kwallo sama da biyu a raga ba a wasa 15 da ta kara a gasar cin kofin Afirka.
Kwallo biyu kacal Equatorial Guinea ta zura a raga daga 11 a Afcon a farkon minti na 45.