fidelitybank

Najeriya za ta dawo ragamar ta idan Tinubu ya daure a kan gyara – JAGG

Date:

Kungiyar hadin gwiwa mai fafutukar ganin an gudanar da shugabanci nagari, JAGG, ta ce Najeriya na kan turbar farfadowa, idan har shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar kawar da irin kudaden da ake barnatarwa wajen tafiya-tafiye.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Mista Abdulwaheed Odunuga ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Laraba a Legas.

Yana mai da martani ne kan umarnin shugaban kasar nan ya yanke adadin jami’an da za su raka shi da sauran manyan jami’an gwamnati a duk wata tafiya ta kasashen waje.

Ya ce ’yan Najeriya sun sha wahala sosai saboda dimbin almubazzaranci a harkokin mulki da kuma a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati.

“Abin farin ciki ne kuma za mu so mu yaba wa shugaban kasa kan wannan mataki.

“A wajenmu, ba wai yana rage kudin gwamnati ba ne, sai dai yana rage almubazzaranci, kuma bai kamata a takaita tafiye-tafiye zuwa kasashen waje kadai ba.

“Idan shugaban kasa zai iya rage wadannan sharar gida ina da kwarin gwiwar cewa ba za mu bukaci lamuni don samar da kasafin kudin ba,” in ji Odunuga.

Yayin da yake bayyana matakin a matsayin mai mahimmi kuma abin lura, Odunuga ya ce an yi shi ne da nufin rage kashe kudaden da ake kashewa a kan takardun shaida da alawus-alawus.

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp