Babban Fasto na Dunamis International Gospel Center, Dokta Paul Enenche ya ce, daukakar Najeriya za ta dawo nan ba da dadewa ba.
Bawan Allah da ya ke jawabi yayin da ya jagoranci mambobinsa wajen yi wa al’ummar kasar addu’a a ranar Laraba, ya ce, nan ba da dadewa ba kasar za ta girgiza duniya baki daya domin al’amura za su canja.
Ya ce, kudin Najeriya, Naira, zai dawo da karfinsa idan aka kwatanta da dalar Amurka, yana mai jaddada cewa fasfo din kasar ma zai samu daraja nan ba da dadewa ba.
Ya ce, “Najeriya za ta sake bunkasa, yawon bude ido zai sake bunkasa a kasar nan. Abubuwan ma’adinai da ba mu taɓa gani ba, za su tashi daga wannan ƙasa.
“Lokaci zai zo da mugaye za su yi wuya su rayu a nan, ba za su yi maganar kafa mulki ba.


