Super Eagles ta koma matsayi na biyu a cikin rukuni na A da maki 4 bayan ta doke mai masaukin baki Cote d’ivoire da ci daya da nema.
Dan wasan bayan Najeriya, Troost-Ekong ne ya zura kwallo a ragar Cote d’ivoire daga bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Yanzu haka Equitorial Guinea na da maki 4 sai Najeriya na da maki 4 sai Cote d’ivoire na da maki 3, yayin da Guinea ba ta da maki ko daya.


