Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin “mutumin da ya ƙarar da rayuwarsa wajen nuna kishin ƙasa da haɗin kan ƙasarmu”.
“Najeriya ta yi rashin dattijo wanda ya ɗauki ɗawainiyar shugabanci a lokutan fargaba da na nasara, wanda kuma ba za a manta da sadaukarwarsa ba a tsawon lokaci,” kamar yadda Atiku ya bayyana cikin wata sanarwa a shafukan sada zumunta.
Ya kuma yi addu’ar “Allah ya yafe masa kurakuransa kuma ya ba shi Aljannar Firdausi”, sannan ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa.
Atiku ya yi hamayya da Buhari a takarar shugabancin Najeriya a lokuta daban-daban, ciki har da na 2019 lokacin da Buhari ke neman wa’adi na biyu.