Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a matsayin rashi da Najeriya, ba ga iyalinsa kaɗai ba.
Ya kuma ce ”ana buƙatar kwarewar duk mutanen da suka samu damar jagorantar kasar nan a baya domin fitar da kasar a cikin halin da take ciki.”
Obasanjo ya kuma ce Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa ga Najeriya, kuma ya yi adduar Allah ya yafe masa kurakurensa ya kuma a aljannah ce makomarsa.