Najeriya ta yi nasara a karar da ta daukaka kan wani hukunci da ke neman ta biya diyyar dala biliyan 11 ga wani kamfanin kasashen waje bayan rushewar wata kwangilar shimfida bututun iskar gas.
Kamfani P&ID mai hedikwata a Virgin Islands na Birtaniya ne ya kai Nijeriya kara a kotun sasanta rikicin kasuwanci, inda ya nemi diyyar kudin da suka kai kashi daya cikin uku na asusun ajiyar kasashen wajen kasar.
Mai shari’a Robin Knowles ya karbi bahasin kalubalantar hukuncin farko da Najeriya ta yi a wani hukunci da ya gabatar ranar Litinin.
“Ban amince da dukkan zarge-zargen da Najeriya ta yi ba,” alkalin ya fada a hukuncin da ya yanke. Sai dai ya kara da cewa hukuncin kotun sasanta rikicin kasuwanci “an same shi ne ta hanyar damfara kuma hanyar da aka same shi, ya saba da manufar aikin gwamnati”.
A shekara ta 2010 ne, Najeriya ta bai wa kamfanin Process & Industrial Developments (P&ID) kwangilar aikin ginawa da gudanar da wata tashar sarrafa iskar gas tsawon shekara 20 a kudancin najeriya, a wani bangare na wani babban shirin hako dumbin arzikin iskar gas da Allah ya hore wa kasar.
Sai dai bayan rushewar yarjejeniyar, kamfanin P&ID ya garzaya gaban kotun sasanta rikice-rikicen kasuwanci da ke London a 2017, wadda ta yanke hukuncin cewa Najeriya ba ta gaskiya kuma ta biya kamfanin dala biliyan 6.6 na asarar da ya yi.
Kudin dai ya yi ta karuwa har zuwa sama da dala biliyan 11 saboda kudin ruwa.
Kiyasi na cewa kudin ya ninka har sau 10 a kan kasafin kudin Najeriya na fannin lafiya na 2019.
Lauyoyin Najeriya sun ce kasar ta tsinci kanta ne a cikin “wata makarkashiyar cin hanci da damfara” daga kamfanin P&ID, wanda suka ce ya bayar da toshiyar baki ga manyan jami’an gwamnati don samun kwangila, daga nan kuma sai ya rika bayar da rashawa ga lauyoyin kasar don samun takardun sirri na hukuma a lokacin shari’ar.
P&ID ya musanta cewa ya samu kwangilar ne ta hanyar ba da toshiyar baki ko ya rika bayar da cin hanci ga lauyoyin Najeriya a lokacin sauraron shari’ar, inda ya dora alhakin rushewar yarjejeniyar iskar gas din a kan rashin kwarewar cibiyoyin gwamnati da ke da alhakin tafiyar da shari’ar.