Sabon shugaban Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa ta (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce an yi asarar naira tiriliyan 2.9 ta hanyar rashin gaskiya a harkar kwangiloli da zamba wajen sayan kayayyakin gwamnati a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga Sanatoci a yayin tantance shi domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC ranar Laraba.
Ya ce adadin kuɗin ya isa a biya kuɗin gina tituna na aƙalla kilomita 1,000, da gina manyan makarantu kusan 200, da kuma ilimantar da yara kusan 6,000 daga matakin firamare har zuwa jami’a a kan Naira miliyan 16 ga kowane yaro.
Da yake ƙarin haske game da hurumin binciken hukumar, Olukoyede – da Majalisar Dattawan ta tabbatar bayan tantancewar – ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban EFCC yana da ‘yancin gudanar da bincike ga kowa a ƙasar.
Ya kuma yi alƙawarin rashin saɓa ƙa’ida a gudanar da aikinsa, yayin da ya sha alwashin yin aiki da al’ummar Najeriya tare da tabbatar da gaskiya da kuma ɗaukar matakan kariya don rage ƙararrakin da aka daɗe ana yi.


