Hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden da aka samu daga ma’adanan man fetur, NEITI, ta ce, Najeriya ta yi asarar gangar mai miliyan 619.7 da kudinsu ya kai naira tiriliyan 16.25 daga 2009 zuwa 2020.
A wata sanarwa da mai magana da yawunta, Obiageli Onuorah, ta fitar a yammacin ranar Laraba ta ce Najeriya na asarar danyen mai saboda yadda ake sace shi da asarar a wani abu da ta kira yi wa kasar zangon kasa.
Jaridar the Punch a Najeriya ta rawaito cewar hukumar ta NEIT ta ce ta gano hakan ne a wasu bayanai da ta tattara daga wasu matsakaitan kamfanoni takwas da ke suka yi aiki akansa tsawon shekaru.
Ta ce ta yaba wa matakin gwamantin ta Najeriya na samar da wani kwamiti na musamman da kan lura da yadda ake sace danyen man.