Babban Manajin Darakta na Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), Mele Kyari, ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar dala biliyan 1.5 tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2022, sakamakon satar danyen mai da aka yi a kasar.
Kyari, wanda yake zantawa da ‘yan kwamitin majalisar wakilai kan albarkatun man fetur a ranar Alhamis a Abuja, ya kuma bukaci a kafa kotuna na musamman da za su gudanar da shari’ar satar danyen mai, barna da ayyukan matatun man kasar ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kamfanin na NNPC, ya kuma yaba da matakin da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya dauka na dakile ayyukan barayi da masu gudanar da ayyukan matatun mai a jihar.
Kyari, wanda ya nunawa ‘yan majalisar ta hanyar bidiyo da hujjoji na hoto da kuma irin barnar da aka yi wa bututun mai, ya kuma koka da yadda wannan mummunar dabi’a ta haifar da mummunan tasirin tattalin arziki wanda a cewarsa, hadin gwiwar hukumomin tsaro da kuma NNPC ke tafiyar da shi da sauran masu ruwa da tsaki na masana’antu da masu gudanarwa za su yi abin da ya dace.