Najeriya ta karɓa tallafin allurar riga-kafin maleriya 846,000 samfurin R12/Matrix-M daga hukumar kula da riga-kafi ta duniya wato GAVI domin yaƙi da cutar maleriya.
“Riga-kafin zai taimaka mana wajen yaƙi da cutar maleriya, da rage mace-mace a tsakanin ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara biyar da kashi 13, da rage zuwa asibiti da kashi 22,” in ji Dokta Muyi Aina, babban daraktan hukumar kula da lafiya a matakin farko.
Kamar yadda ƙididdigar hukumar lafiya ta duniya WHO ta nuna, Najeriya ce kan gaba a cutar maleriya a duniya, inda ƙasar ke da kashi 27 na cutar a duniya, kuma take kan gaba wajen yawan mace-mace a sanadiyar cutar.
Za a fara riga-kafin ne a watan Nuwamba a jihohin Kebbi da Bayelsa, ina cutar ta fi ƙamari, inda za a yi wa ƙananan yara masu wata biyar zuwa 16, inda za a musu allura huɗu domin kariya.
Za a faɗaɗa cutar zuwa jihohi 19 a shekarar 2025, sannan kuma akwai shirin ba masu raino da shugabannin al’umma da ma’aikatan jinya.
WHO ta amince da riga-kafin R12.Matriz-M ne a watan Disamban 2023 domin amfani da shi ga ƙananan yara.