Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta ƙasa ta bayar da rahoton cewa, ta samu gagarumin ci gaba wajen aiwatar da matsayar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2018 kan yaki da cutar tarin fuka (TB) a Najeriya.
Dakta Chukwuma Anyaike, Daraktan kiwon lafiyar jama’a na ma’aikatar ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da masu ruwa da tsaki kan cutar tarin fuka a Abuja.
Cutar ta TB na ci gaba da zama wani babban kalubale a fannin kiwon lafiyar al’umma a Najeriya, inda kasar ke cikin jerin kasashe 10 na duniya da ke fama da matsalar tarin fuka.
Dakta Anyaike, wanda Dr. Urhioke Ochuko ya wakilta, ya bayyana cewa adadin waɗanda suka kamu da cutar tarin fuka kuma da aka yi wa magani sun ƙaru a Najeriya.
“Mun gano karin mutane sama 285,000 da suka kamu da cutar, sannan an cimma kashi 60 cikin 100 na burin da aka sa gaba wajen gano masu dauke da cutar a shekarar ta 2022,” in ji shi.
Bugu da kari, Najeriya ta yi kokarin karfafa tsarin kiwon lafiyarta, ta hanyar horar da ma’aikatan kiwon lafiya da kafa karin cibiyoyin kula da masu dauke da cutar tarin fuka.
Ya kara da cewa “Rigakafin cutar tarin fuka ya kuma inganta tun daga 2018.”
Ya ce gwamnati ta nuna himma a siyasance don magance tarin fuka kuma ta kara yawan kudade tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa.
Duk da haka, Dr. Anyaike ya lissafo ƙalubalen da ake fuskanta da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da ƙarancin gano masu cutar tarin fuka cikin yara, da rashin isassun rajistar masu fama da cutar.
Ya bukaci mahalarta taron da su nemo wata damar da za a kara zuba jari a fannin maganin tarin fuka da sabbin dabarun samar da kudade don bayar da tallafi kan cutar ta tarin fuka.


