Gwmanatin Najeriya ta nemi izinin takwararta ta Hungary izinin saukar jirgin da zai ɗebo ‘yan Najeriya da suka shiga ƙasar daga Ukraine sakamakon yaƙi.
A cewar BBC, yanzu babu jimawa Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce, ya tattauna da takwaransa na Hungary.
Gwamnatin Najeriya ta ce, kashin farko na ‘yan ƙasar da za a kwaso za su sauka a yau Alhamis, inda za a ɗebo su daga Hungary da Poland da Romania.