Zakarun Najeriya, Delta Queens, za su kara da USFA ta Burkina Faso da Beninoise, Sam Nelly a rukunin A na WAFU Zone B na neman shiga gasar cin kofin zakarun mata na CAF na 2023 ta kwallon kwando.
A ranar Juma’a ne aka fitar da jadawalin gasar.
Ampem Darkoa na Ghana da Amis Du Monde na Togo da kuma Atletico FC ta Ivory Coast a rukunin B.
Filin wasa na Samuel Ogbemudia Benin City ne zai karbi bakuncin dukkanin wasannin da za a buga a gasar.
Za a gudanar da gasar ne daga ranar 20 ga watan Agusta zuwa 31 ga watan Agusta.
Bayelsa Queens ta Najeriya ce ke rike da kofin gasar.