Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka.
Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi.
Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015.
Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.