Super Eagles ta Najeriya a ranar Lahad ta kasa doke Equatorial Guinea a wasan da kungiyoyin biyu suka fafata a gasar cin kofin Afrika ta 2023 a Cote d’Ivoire.
An tashi wasa 1-1 a filin wasa na Olympics.
Ivan Salvador ne ya farkewa Equatorial Guinea 1-0 a minti na 36 da fara wasa.
Sai dai kuma Victor Osimhen ya dawo da bugun daga kai sai mai tsaron gida da kai.
Kungiyoyin biyu sun kasa cin kwallo a zagaye na biyu, inda suka tashi da maki daya kowacce.
Wasan Najeriya na gaba zai fafata da mai masaukin baki ranar Alhamis.