Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kare ma’aikanta daga barazanar hare-hare a faɗin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan wani sojan Najeriya ya bude wuta a wani sansanin sojoji da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar.
Sojan ya kashe ɗan uwansa soja ɗaya da kuma wani ma’aikacin agaji, sanna ya raunata wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tana mai cewa sojojinta da ke wurin sun yi nasarar kashe sojan da ya yi ta’asar.
Sanarwar ta ce matukin helikwaftan ba ya cikin wani garari, akwai alamun samun sauki a gareshi.