Tawagar ‘yan matan Najeriya ta kai matakin zageyen ‘yan 16 a gasar Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasar da shekara 20 da ke gudana a ƙasar Columbia.
Hakan na zuwa ne bayan da Falconets ta caskara Venezuela da ci 4-0 a wasan ƙarshe na cikin rukuni.
Tun da farko ‘yan matan Najeriyar sun samu nasara kan Jamhuriyar Koriya da ci 1-0, inda kuma ta yi rashin nasara a hannun Jamus da ci 3-1.
A yanzu Falconets za ta fafata da Japan ko Austria a zagen ‘yan 16, ranar 13 ga watan Satumban da muke ciki.