Najeriya ta hana ofisoshin jakadun ƙasashen waje amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje, domin gudanar da ayyukan neman takardun biza da sauran harkokinsu.
Najeriya da ke fama da matsalar karyewar kuɗin ƙasar wato naira b- ta umarci ofisoshin jakadun ƙasashen wajen su riƙa amfani da kuɗin ƙasar wajen gudanar da hada-hadarsu.
Hukumar Yaƙi da ya yi wa Tattalin Arzikin Najeritya Ta’annati ta EFCC, ta ce an ɗauki matakin ne domin magance mamayar da dala ta yi wa harkokin tattalin arzikin ƙasar, tare da karyewar darajar kuɗin ƙasar, wato naira.
EFCC ta bayyana hada-hada da kuɗin ƙasashen waje da ake yi a ofisoshin jakadun wajen a matsayin wata barazana ga tattalin arzikin ƙasar, da ƙarfi ko kimar ƙasar.
Abaya-bayan nan Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin kayyaki tare da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da ba a taɓa gani ba, musamman a shekarar da muke ciki.