Ƙasar Poland ta buƙaci Najeriya ta saki wasu yan ƙasarta da ta kama a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar.
Hukumar tsaron farin kaya ta kasar ce ta kama mutanen bisa zargin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zangar a jihar Kano.
A yanzu dai haka tun a lokacin jami’an tsaro suka tura su zuwa Abuja, domin cigaba da gudanar da bincike a kan su.