Wani babban Lauyan Najeriya Femi Falana, ya yi kira ga ‘yan kasuwa su dage wajen yin hada-hadar kasuwanci da Naira, ciki har da amfani da ita wajen biyan kuɗin kayan da ake shiga da su ƙasar daga China.
Tashar talbijin ta Channels ta ambato Falana na tunasar da ‘yan Najeriya game da yadda gwamnatin ƙasar da China suka ƙulla yarjejeniyar musayar kuɗi shekara biyar da ta gabata.
Ya yi nuni da cewa, cinikin wanda ya kai RMB biliyan 16 ko kuma Naira biliyan 720, an yi shi ne don samar da isassun kuɗaɗen gida ga masu masana’antu na Najeriya da China da sauran ‘yan kasuwa, tare da rage matsalolin da ake fuskanta wajen neman dalar Amurka.
An kuma tsara musaya tsakanin ƙasashen biyu don inganta sauri da sauƙaƙawa, da yawan hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Lauyan ya ƙara da cewa, duk da tabbatar da cewa yarjejeniyar har yanzu tana nan daram kuma tana aiki, amma har yanzu babban bankin Najeriya bai bar ‘yan ƙasar su yi kasuwanci a kasar China ta hanyar amfani da naira ba.
Lamarin da ya ce ya zama dole, inda ya bukaci ‘yan kasuwar Nijeriya su dage su rika hada-hadar kasuwanci da naira, ciki har da biyan kuɗin kayan da ake shiga da su daga kasar China.


