Hukumar kula da harkokin samar da makamashi ta Najeriya, wato Energy Commission Of Nigeria, ta ce ta yunkuro a ƙoƙarin kawo sauyi game da yadda ake sama wa al’ummar ƙasar wutar lantarki.
Hukumar ta ce ta ɓullo da wasu sabbin tsare-tsare da za su inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin, waɗanda suka haɗa da hasken rana da iska da sauransu.
Shugaban hukumar, Dokta Mustafa Abdullahi, ya ce Najeriya na samar da megawatt 12,000 na wutar lantarki, amma 5,000 kaɗai ke isa ga gidajen mutane.
Ya ce ana buƙatar megawatt 40,000 na wutar lantarki kafin ta isa al’ummar Najeriya.