Tsohon gwamnan Sokoto kuma Sanatan da ke wakiltar Kudancin Jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya ce, Najeriya na cikin mummunan halin da take buƙatar a kai mata ɗaukin gaggawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Tambuwal na ce akwai buƙatar haɗa hannu tare domin ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Da aka tambaye shi game da hakin da ƙasar ke ciki, Tambuwal sai ya ce “da na tafi hutun magana da manema labarai. Ina sane na gwammace na yi shiru kimanin wata tara kan halin da muke ciki.
“Yana da na shiga na shiru, yanayin da zuciyata take ciki kenan, Kawai na hakura da magana ne. Idan ka tsinci kanka cikin abu, kuma wani yanayi da ba a yi tsammani ba ya faru, dole ka yi shiru.”.
Amma a cewarsa duk mai son ya ji yanayin da Najeriya ke ciki ya je ya tambayi mutanen ƙasar.
Ya ce ba sai mutum ya je nesa ba, kamata ya yi ya tambayi kansa yanayin da ake ciki. “Najeriya na cikin mawuyacin hali. Tana buƙatar ɗaukin gaggawa. Wannan nauyinmu ne babu magnar jam’iyyar siyasa ko addini ko yare wajen aikin ceto ƙasarmu”.
Tsohon kakakin ƙasar ya shawarci ‘yan jarida da su riƙa gayawa shugabanni gaskiya kan yanayin da Najeriya ke ciki.


