Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana fatansa na cewa ko wane hali da yanayin da ake ciki, komai zai daidaita a Nijeriya.
Obasanjo, wanda ya bayyana hakan a wani taron Crusade na Duniya da Cocin Deeper Life Bible Church ta shirya, a Abeokuta a ranar Talata, ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance da bingaskiya ga Allah.
Tsohon Shugaban kasar ya ce, idan aka yi la’akari da halin da al’amura suke ciki, Nijeriya da ma duniya baki daya na bukatar ɗaukin Allah.
Idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a garuruwanmu, jihohinmu, kasarmu, yankinmu na Afirka ta Yamma, nahiyarmu da duniyarmu, duniyarmu ta bukaci a yi yaki irin wannan.
“Wasu mutane sun zarge mu, Kiristoci da ‘ addini’ ba tare da ruhi ba. Hakika, wannan shi ne matsayin duniya har a lokacin Yesu Kristi, amma ya kamata mu daina bege? A’a.
Najeriya na bukatar irin wadannan mutane masu gaskiya a halin yanzu.