Fadar shugaban kasa ta ce yayin da shekarar 2023 ke gabatowa, ‘yan Najeriya na bukatar su zabi wani shugaba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai iya kawar da cin hanci da rashawa a kasar.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis ta cikin shafinsa na Facebook, mai suna, PMB AND THE NDDC wanda ya kasance martani ga binciken da ake yi a hukumar raya yankin Neja Delta.
Adesina ya bayyana cewa, an kwashe sama da shekaru 15 a na cin hanci da rashawa a hukumar ta NDDC, kuma shekaru biyu ne kawai aka fara samun sauki.
Ya ce, “Hukumar Neja-Delta (NDDC) wata hukuma ce, mai shiga tsakani da aka kirkira, domin ci gaban yankin da ake hako mai a kasar nan.
“To, ana nufin ya zama hukumar shiga tsakani, amma abu ɗaya a bayyane yake. Duk da daruruwan biliyoyin Nairori da aka zuba cikin shekaru 20 da suka gabata, maganar gaskiya ta kasance cikin aljihun wasu zababbun mutane, maimakon yankin da kuma rayuwar al’umma gaba daya”. A cewar Adesina.