Tsohon ministan matasa wasanni da al’adu, Solomon Dalong, ya shawarci ‘yan siyasar da suka haura shekaru 65 da su hakura da neman kujerar shugabancin kasa su barwa matasa.
Dalong ya ce kamata ya yi su mayar da hankali wajen zama sanatoci a majalisar dokokin tarayya, sakamakon tsufa da masu neman kujerun ke da shi.
Ya ce“Matasa masu jini a jika ne ya kamata su dare kujerar shugaban kasa, kamata ya yi duk dan siyasar da ya haura shekaru 65 ya duba yiwuwar zuwa majalisar dattawa, sannan ya hakura da kudirin yin takarar kujerar shugaban kasa”. In ji Dalong.
Sahara Reporters ta rawaito cewa, tsohon ministan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jadadda cewar, a yanzu Najeriya na bukatar mutum mai ji da karfi a matsayin shugaban kasa maimakon tsoffin mutane da suka nuna kwalamar su.