Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce babu lokacin da ya fi dacewa a yi wa Najeriya addu’a kamar a watan Ramadan.
A cewar sa, kasar na bukatar addu’o’in neman taimakon Allah.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Abdullahi Krishi ya fitar a lokacin da yake taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murnar ganin watan Ramadan.
Abbas ya bukaci ba Musulmi kadai ba, har ma da daukacin ‘yan Nijeriya da su yi addu’a domin hadin kan kasar nan, kuma gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu damar magance dimbin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su rika tunawa da wadanda wasu kungiyoyi masu dauke da makamai suka yi garkuwa da su a fadin kasar nan kuma suka ci gaba da tsare su a cikin addu’o’insu.
Ya ce, “Allah Ta’ala Ya karbi addu’o’inmu da addu’o’inmu a matsayin ibada, ya kuma ba mu damar zagayawa cikin wannan lokaci mai cike da tashin hankali na al’umma”.