Najeriya na buƙatar naira tirliyan 21 don cike giɓin da take da shi a ɓangaren gidaje, duk da ƙoƙarin matakan gwamnati uku.
Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana haka a Sokoto, lokacin ƙaddamar da bikin gina rukunin gidaje guda 500 da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Kashim Shettima na yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto, saboda ƙoƙarinsa wajen magance buƙatun gidaje a tsakanin al’ummar jihar, ya ma nunar da cewa giɓin gidajen da ake da shi a Najeriya, wani babban ƙalubale ne.
”Najeriya na da giɓin gida miliyan 28 kuma za mu buƙaci naira tirliyan 21 don cimma buƙatun gidajen da muke da su. Wannan mataki da gwamna ya faro, babban abin yabawa ne kuma ya cancanci koyi daga sauran gwamnatocin jihohi.
Tun da farko, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto na gina rukunin gidajen ne saboda ma’aikata, kuma za a sayar musu da su ne da zarar an kammala aikin a kan tsarin ɗan haya ya mallaka.


