Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya tattauna da masu ruwa da tsaki da wakilan jam’iyyar APC a jihar Jigawa, inda dan takarar shugaban kasa ya jaddada cewa, kasar nan ta cancanci mafi kyawu wajen ganin ya gaji kujerar Buhari.
Ziyarar da Osinbajo ya kai Jigawa na ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da wakilan jam’iyyar gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Maudu’in sakon mataimakin shugaban kasar a Dutse babban birnin jihar Jigawa, shi ne cewa, ya kamata a yanke hukunci kan zaben 2023, bisa la’akari da maslahar Najeriya.