fidelitybank

Najeriya na asarar sama da dala biliyan 1.1 saboda cutar Maleriya – Ministan Lafiya

Date:

Ministan lafiya Farfesa Muhammad Pate, ya ce arziƙin da ƙasar nan take asara a shekara sakamakon cutar zazzaɓin cizon sauro (maleriya) ya zarta dala biliyan 1.1.

Pate ya bayyanna hakan ne kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, yayin ƙaddamar da taron bayar da shawarwari da tuntuɓa kan yaƙi da cutar ta maleriya a Najeria, wanda aka yi a Abuja.

A wata sanarwa da mataimakin darektan yaɗa labarai na ma’aikatar, Alaba Balogun, ya fitar a yau Talata, ya ce Farfesa Pate ya ce maleriya ba matsala ce ta rashin lafiya ba kaɗai ta zama matsala ga tattalin arziƙi da cigaba wadda ya kamata a ɗauki ƙwararan matakan yaƙi da ita.

Ya ce, maleriya na ci gaba da gagarumar illa a kan Najeriya, inda take da kashi 27 cikin ɗari na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a duniya, da kuma kashi 31 cikin ɗarin na yawan mutanen da ke mutuwa a duniya a dalilinta .

Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ce ta fi fama da matsalar wannan cuta, inda a 2022, sama da yara ‘yan ƙasar 180,000 ‘yan ƙasa da shekara biyar suka mutu a sanadiyyar cutar – ”wanda wannan abu ne da za mu iya kauce wa.” In ji ministan.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp