fidelitybank

Najeriya da kamfanin Google za su daƙile hotunan tunziri da ake yaɗa wa – Lai

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da kamfanin intanet na Google, wajen daƙile wasu tasoshin yaɗa hotunan bidiyo a dandalin Youtube da suke ƙoƙarin yi wa gwamnati ƙafar ungulu.

Ministan yaɗa labaran ƙasar ne ya bayyana aniyar gwamnatin a wata ganawar da ya yi da masu kamfanin Google. In ji BBC.

Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da aniyar gwamnatin Najeriyar, a wata ganawar da ya yi da wani ayarin kamfanin na Google a Abuja a jiya.

Ya ce, irin wadannan tasoshi ba su da wani aiki sai yaɗa labaran ƙarya da cusa gaba a tsakanin al’ummar ƙasar.

Cikin wata sanarwa, Alhaji Lai Mohammed ya ce, zai so kamfanin Google ya duba hanyoyin da zai yi maganin wasu tasoshi da na wasu kungiyoyin da gwamnati ta haramta wanzuwarsu ta hanyar toshe su da adireshinsu na sada bayanai ko saƙonni da sauran hanyoyin da suke bi suna yada manufofinsu ta intanet.

Ministan ya yi misali da ƙungiyar IPOB, mai fafutukar kafa ƙasar Biafra, wadda ya ce haramtacciya ce, kuma shafin google shi ne danadalin da mafi yawan mabiyanta ke bibiya, kuma ta nan take yaɗa aniyarta ta haddasa husuma da wargaza ƙasa.

A cewar Ministan, Najeriya na cikin kasashen duniya, waɗanda mutanensu ke gaba-gaba wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani irin su Google da Facebook da Tik-tok da Twitter da kuma Whatsapp, wadanda adadinsu ya kai fiye da miliyan dari.

Alhaji Lai Mohammed ya ce, irin waɗannan kafofin suna taimakawa sosai, saboda suna bai wa ƴan Najeriya damar hulɗa da juna da musayen ra’ayi, har ma da gudanar da harkokin kasuwanci da na siyasa.

Amma kamar yadda ya koka, wasu ɓata-gari na amfani da su wajen yi gwamnati zagon-ƙasa.

Jagoran ayarin kamfanin na Google, Mr Charles Murito ya ce, kamfanin ya fito da wani shiri na horar da ƴan kasa a kan yadda za su dinga nazarin abubuwan da ake wallafawa ko yadawa ta intanet.

Hakan zai sa su fahinci abubuwan da ke da illa don ankarar da kamfanin, yana cewa shi kamfanin nasu ba ya goyon bayan masu yaɗa abubuwan da za su haddasa tashin hankali.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp