Najeriya da Jamus sun amince da kara yawan ƙarfin wutar lantarki watts miliyan 12, ta hanyar shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa (PPI).
Shirin samar da wutar lantarki wanda gwamnatin tarayya za ta samar da rancen bashi zuwa kasashen waje a halin yanzu da wasu bankunan kasar Jamus ke yi wa Najeriya, zai lakume kusan dala miliyan 60 kuma zai hada da siyan tiransifoma 10 da tashoshi guda 10.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, duk sun jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Juma’a a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya Climate Conference (COP28) a Expo City.
Manajan Daraktan Kamfanin Lantarki na Gwamnatin Tarayya, Kenny Anue ne ya sanya hannu a madadin Najeriya yayin da Nadja Haakansson, Manajan Darakta (Africa) Siemens AG, ya sanya hannu a madadin Siemens.
Anue ya jaddada kudirin shugaban kasa, Tinubu na inganta samar da wutar lantarki a Najeriya, inda ya jaddada cewa ya nanata cewa samar da ababen more rayuwa na da matukar muhimmanci ga sauye-sauyen da ake yi.
Ya bayyana cewa makamashi da kudade suna tsakiyar manufar sake fasalin tattalin arziki na gwamnati kuma PPI, ta hanyar tsarawa, ta ƙunshi sassan biyu tare da goyon bayan abokan hulɗa, Siemens Energy da masu kudi da gwamnatin Jamus ke goyon bayan.
Da yake jawabi ga shugaban kasa, Anue ya ce: “Ya shugaban kasa, tare da kwazonka da jajircewarka ta hannun Maigirma Ministan Wutar Lantarki, yanzu muna neman yin amfani da ko kuma aiwatar da abin da ya rigaya ya kasance wani shiri mai amfani a shirin ikon shugaban kasa ta hanyar wannan yarjejeniya mai karfi a yau.”


