Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA da takwararta ta India, sun amince da ƙara haɗa kai wajen yaƙi da safarar muyigun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu.
Hakan na cikin batutuwan da shugabannin hukumomin, Birgediya janar Buba Marwa mai ritaya da Mista Anurag Garg su ka amince da su a lokacin wata tattaunawa da suka yi ta intanet.
Sun ce za su fi mayar da hankali ne kan yadda ake shigar da haramtattun magunguna kamar tramadol da magunguna masu hodar ibilis cikin Najeriya daga Indiya.
Buba Marwa ya ce irin waɗannan ƙwayoyi na da illa matuƙa kan lafiya da tsaro a ƙasashen biyu, ya kuma ce akwai buƙatar hukumomin biyu su ƙara ƙarfafa alaƙarsu bisa la’akari da yarjejeniyar fahimta da suka sanya wa hannu a 2023.
Ya kuma buƙaci hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Indiya NCB ya taimaka wajen bai wa jami’ansa horo na musamman.
Najeriya na daga ƙasashen duniya da suka yi ƙaurin-suna wajen sha da safarar miyagun ƙwayoyi, abin da ya sa gwamnatin ƙasar ɗaukar matakai daban-daban ciki har da kafa ita hukumar ta NDLEA.