Gwamnatin Najeriya ta ƙulla yarjejeniya da ƙasar Cuba, domin samar da abinci da fasahar ci gaban harkokin noma.
Ministan albarkatun noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin Najeriya a lokacin taron ƙaungiyar ƙasashen G-77 ta ƙasashe masu tasowa da ka gudana a birnin Havana na ƙasar Cuba.
Cikin saƙon X da mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima – wanda ke wakiltar shugaban ƙasar a taron – ya wallafa ya ce, yarjejeniyar za ta ƙarfafa dangantakar harkokin noma tsakanin ƙasashen biyu a fannin noma.
Sanata Abubakar Kyari ya yaba wa gwamnatin Cuba kan ƙulla yarjejeniyar, yana mai cewa duka ƙasashen biyu na da buri iri ɗaya kan al’umominsu.
Ministan ya nuna jin daɗinsa kan wannan yarjejeniya da ya ce za ta taimaka wajen magance tarin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a ɓangaren abinci da harkokin noma.
Ya ce Najeriya a shirye take ta haɗa hanu da Cuba a ɓangarorin kiwon kaji da na manyan dabbobi da kiwon kifi.
Ɓangarorin da yarjejeniyar za ta mayar da hankali sun haɗar da batun samar da magungunan dabbobi, da samar da riga-kafin dabbobi da yi wa dabbobi baye da sauran fannoni.


