Kididdigar zaman lafiya ta duniya ta 2022 ta sanya Najeriya a matsayi na 143 a cikin kasashe da yankuna 163 masu cin gashin kansu, bisa ga matakin zaman lafiya.
Najeriya ta koma matsayi uku a kan teburi daga matsayi na 146 da ta kasance a bara.
Sauran kasashen da ke kan gaba a matsayi na Najeriya sun hada da Mauritius 28; Ghana 40; Gambiya 45; Saliyo 50; Equatorial Guinea 59; Malawi 65; Senegal 70; Maroko 74; Rwanda 72; Laberiya 75; Gabon 75; Angola 78; Lesotho 100; Madagascar 8; Mozambique 122; da Namibiya 68.
Sauran su ne Zambia 56; Tunisiya 85; Tanzania 86; Nijar 140; Burundi 131; Jamhuriyar Benin 105; Botswana 48; Jamhuriyar Kongo 111; Ivory Coast 108; Kamaru 142, Djibouti 113, Algeria 109; Afirka ta Kudu 118; Masar 126, Eritrea 132, Guinea 123, Guinea Bissau 110; Chadi 136; Togo 102; Uganda 121 sai Zimbabwe 127.