fidelitybank

Najeriya ce ta 140 cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya

Date:

Najeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024, in ji ƙungiyar Transparency International.

A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa.

Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙasashe 180 na duniya ya yi amfani da masana da ƴan kasuwa wajen tantance matsayin kowace ƙasa.

Ma’auni tantance munin cin hancin ya kama ne daga maki sifili zuwa 100, inda sifili ke nufin mummunan matsalar cin hanci yayin da 100 ke nufin rashin matsalar baki ɗaya.

Rahoton ya yi la’akari ne da ƙarfin hukumomi a ƙasashen, da inganci zaɓe da kuma ɗabi’ar gwamnati.

Transparency International ta ce Najeriya tare da wasu ƙasashe kamar Uganda, Mexico, Madagascar, Iraq da Kamaru sun samu maki 26 ne cikin 100.

Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Venezuela na cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a duniya.

Transparency ta ce cin hanci babban barazana ce ga sauyin yanayi. Ta ce hakan yana kawo cikas wajen batun rage fitar da gurɓataccen iska da masana’antu ke yi.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp