fidelitybank

Najeriya ce ƙasa ta biyu a duniya da ƴan ƙasar suka shiga Birtaniya aikin yi

Date:

Wani rahoto da ofishin kula da ƙididdiga na Birtaniya ya fitar, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu mafi yawan mutanen da suka yi tururuwa zuwa Birtaniyan a shekara ta 2024.

Alƙaluman rahoton sun nuna cewa ƴan Najeriya 120,000 ne suka kwarara zuwa Birtaniya a 2024.

Lamarin na nuna cewa ƙasar tana biye da Indiya da ke matsayi na farko a jerin, inda mutanen ta 240,000 suka shiga Birtaniyar.

Rahoton ya ce batun neman aikin yi yana cikin abubuwan da ke sa ƴan Najeriya tururuwar zuwa Birtaniya.

Dakta Ishaku Shitu Al-Mustapha,wani babban malami a jami’ar Canterbury Christ da ke birnin Landan, ya ce neman kyautatuwar rayuwa, kuma su na cikin abin da ya sa ƴan Najeriya ke ƙaura zuwa Birtaniyar.

“Wasu ƴan Najeriya sun gaji da ƙasar, ga rashin shugabanci na gari da kuma rashin albashi mai kyau su ma suna cikin abin da ya ƴan ƙasar ke ficewa daga cikinta,” in ji Dakta Al-Mustapha.

Ya ce samun shugabanni masu kishin ƙasa da kuma tsoron Allah zai sa ƴan Najeriya su rage fita zuwa ƙasashen waje.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp