fidelitybank

Najeriya ce ƙasa ta 3 a duniya da aka fi cin naman Kare

Date:

Wani binciken masana ya bayyana cewar, Najeriya ce kasa ta 3 da aka fi cin naman kare a duniya, bayan kasashen Koriya ta Kudu da Vietnam.

Rahotan binciken da Mathew Nash ya jagoranta wanda Jaridar Premium Times ta wallafa yayi karin haske akan kasashen da kiwon karnuka ke da tasiri da akasin haka a wannan shekara ta 2022.

Rahotan ya ce duk da ya ke ana matukar cin naman karan lokacin bukukuwa a China, kasar bata cikin jerin kasashe 3 na duniya da aka fi cin naman karan kamar yadda binciken da aka gudanar a kasashe 51 ya nuna.

Wannan binciken ya mayar da hankali ne akan kasashen da ake kare hakkin karnukan da kasashen da ake barin karnukan su shiga otel-otel da wadanda ke da isassun likitocin dake kula da su da masu kungiyoyin kare hakin dabbobi da masu fama da barazanar kamuwa da cutar cizon karnukan da kuma wadanda ke da dokar alaka tsakanin dabbobi da mutane.

Najeriya ta zo ta 45 daga kasashe 51 da suka cika mizanin binciken da aka gudanar da maki 44.41, yayin da Italiya ke matsayi na farko sai New Zealand sannan Faransa da Birtaniya da Jamus.

Duk da matsayin Najeriya na zama kasa ta 3 da aka fi cin naman karen, a watan Yulin bara akalla mutane 18,000 suka sanya hannu akan wata takardar korafi inda suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da su haramta cin naman karen da kuma sayar da shi.

Rahoton ya ce, naman karen dai yana da matsayi sosai a wasu jihohin Kudancin Najeriya da suka hada da Akwa Ibom da Cross Rivers da kuma Rivers inda ake masa lakabi da 404.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp