fidelitybank

Najeriya ba za ta sake cin bashi ba – Ministar Kudi

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, ba ta da niyyar sake karɓo bashi a ciki ko wajen ƙasar ba, bayan cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje.

Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙi, Cif Wale Edun ne ya bayyana haka a ƙarshen taron Majalisar Zartarwar Ƙasar na farko ranar Litinin a Abuja.

Ya ce amfanin da aka samu daga cire tallafin man fetur, za a zuba shi a ɓangarori daban-daban da za su taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati da inganta kasuwanci a cikin gida da kuma samun zuba jari daga ƙetare.

Wale Edun ya ce bayan ƙarin kuɗin shigar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, an tsara matakan fitar da tallafin rage raɗaɗi na taƙaitaccen wa’adi da matsakaici da kuma dogon lokacin.

Ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na muradin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki nan da wani ɗan lokaci.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ruwaito ministar masana’antu da kasuwanci da harkokin zuba jari, Doris Uzoka-Anite na cewa tuni har an fara samun masu tayin zuwa Najeriya don zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin ƙasar ciki har da ɓangaren man fetur da iskar gas da lafiya da haƙar ma’adanbai da kuma noma.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp