Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ce ƙasar ba za ta lamunci matsin lambar da Amurka ke yi mata na karɓar ƴan ciranin Venezuela da Amurkan ke son ƙwasa tare da mayar da su Najeriya.
Cikin wata hira da gidan Talbijin na Channels, Yusuf Tuggar ya ce ƙasar na da ”nata matsalolin” don haka ba za ta amince a kawo mata muwaten wata ƙasa ba da aka kora da Amurka.
Matakin na Amurka na zuwa ne kwana biyu bayan da Amurka ta sanar da sauye-sauyen tsarin bai wa ƴan Najeriya bizar masu yawon buɗe ido da ƴan kasuwa, matakin da gwamnatin Najeriyar ta nuna rashin jin daɗinsa.
Gwamnatin Trump dai na ƙokarin kwashe baƙin hauren da suka je ƙasar, musamman baƙaƙen fata domin mayar da su wata ƙasa ta baƙaƙen fata.