fidelitybank

Naira za ta ci gaba da yin nasara a kan dalar Amurka – Shettima

Date:

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bada tabbacin cewa Naira za ta ci gaba da yin tsada idan aka kwatanta da dala.

Shettima ya ce shugaba Bola Tinubu ya fahimci wasan kuma zai tabbatar da cewa Naira ta ci gaba da daraja.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas, karkashin jagorancin shugabanta, Gabriel Idahosa ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.

Wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, ta ruwaito mataimakin shugaban kasar na cewa dole ne Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da kuma tabbatar da hadewar kudaden musaya da dama domin a baya tsarin yana samar da hamshakan attajirai cikin dare.

Ya ce: “Naira ta tafi haywire wasu mutane suna biki amma a ciki muna yi musu dariya saboda mun san cewa muna da shugabanni da za su sauya salon tafiyar.

“Asiwaju ya san wasan, kuma da gaske Naira na karuwa kuma bambancin zai kara raguwa.”

Mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, irin jagoranci da Tinubu ya samar a matsayin gwamnan Legas ya sa harsashin ci gaban da aka samu a jihar.

“A koyaushe za mu gode wa Shugaba Tinubu saboda samar da tsarin ci gaban Legas da muke gani a yau,” in ji shi.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp