fidelitybank

Naira miliyan 44.2 sun yi batan dabo wajen sayen fom din takarar APC

Date:

Jam’iyar APC na binciken yadda Naira miliyan 44.2 suka yi batan dabo ranar Laraba a sakatariyar jam’iyar da ke Abuja.

Batan kudin ya janyo dakatar da sayar da fom din ‘yan takara, musamman ‘yan takarar da ke son tsayawa takarar mukaman ‘yan majalisar wakilai da na dattawa.

Jam’iyyar ta kafa wasu rumfuna, domin sayar da fom din ga masu son tsayawa takara.

Sai dai da misalin karfe 4:15, jam’iyyar ta cire rumfunan kuma ta umarci ma’aikatanta su ci gaba da sayar da fom din a cibiyar gudanar da taruka ta International Conference Centre da ke Abuja.

Jaridar Daily Post ta ce wannan matakin ya biyo bayan bacewar dalar Amurka 75,000 ne wanda yayi daidai da Naira miliyan 44.2.

Wani ma’aikacin jamiyyar da baya son a bayyana sunansa ya ce, an cire rumfunan ne bayan da aka gane kudaden sun yi batan dabo.

Ma’aikacin ya ce “Mun ji cewa wani mutum da yazo sakatariyar jam’iyyar, sai dai saboda yawan jama’a bai iya shiga cikin ginin ba da motarsa. Amma yayin da yake kokarin shiga cikin ginin, mun ji wai wani ambulan da yake dauke da shi wanda dala 75,000 ke ciki ya fadi.”

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp