Yayin da al’ummar musulmin kasar nan suka bi sahun sauran takwarorinsu na duniya domin fara azumin watan Ramadan na bana, shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Malam Jalal Arabi, ya shawarce su da su rungumi jajircewa da imani domin kokarinsu ya samu lada wajen Allah.
A cikin wani sako na watan Ramadan mai taken: Rungumar Juriya da Imani a wannan Ramadan da aka fitar a ranar Litinin a madadin hukumar gudanarwa da ma’aikatan hukumar, ya ce hakan ya zama muhimmi saboda kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da kasar nan ke fuskanta.
“A wannan lokaci mai tsarki na tunani da sadaukarwa, mu a hukumar alhazai ta kasa NAHCON, muna so mu jaddada mahimmancin juriya da imani wajen fuskantar kalubale.
“Alkur’ani ya umurci musulmi da su jure jarabawa daban-daban, inda Allah ya bayyana,” in ji shi
Arabi ya kara da cewa: “Kuma lalle ne za mu jarraba ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da ‘ya’yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri.”
“Hakika kalubale daya ko biyu na iya wanzuwa a tsakanin al’umma amma wani bangare na imanin musulmi shine sanin cewa hikimar Allah tana cikin kowane bangare na rayuwa, gami da lokacin yunwa da wahala, hade da hakuri, rabawa da tausayawa.
“Wata ne a gabanmu lokacin da ake bukatar a tsananta addu’o’in neman taimakon Allah ta kowane fanni na rayuwarmu. Yayin da muka shiga wannan motsa jiki na ruhaniya, bari mu hada kai mu sami wahayi daga bangaskiyarmu ga Allah, mu sami ƙarfin juriya a cikin gwaji.
“Lokaci ne da za mu taru a matsayin al’umma, muna tallafa wa juna ta hanyar kyautatawa, tausayi da fahimta. Ramadan ya zama abin tunatarwa cewa sadaukarwar da muka yi tare da juriya na karfafa alaka mai zurfi da Allah da kuma fahimtar hadin kai,” in ji shi.
Shugaban NAHCON ya karfafawa dukkan musulmin Najeriya kwarin gwiwar rungumar azumin watan Ramadan da zuciya daya, tare da fahimtar cewa kalubale dama ce ta girma da ci gaban ruhi.