fidelitybank

NAFDAC ta yi gargaɗi kan illar shan maganin ƙarfin maza

Date:

Hukumar Tabbatar da  Sahihancin Magunguna da Abinci ta Ƙasa, NAFDAC ta ta yi gargaɗi kan illolin da shan magungunan karfin maza ke haifarwa a jikin ɗan adam.
NAFDAC ta ce shan maganin ƙarfin maza kan haifar da mutuwar fuju’a, ma’ana, mutuwar gaggawa.
Hukumar ta ƙara da cewa magungunan karfin maza kan haifar da cutar ɓarin jiki inda maza za su riƙa shan su domin su burge matan da su ke saduwa da su.
Darakta-Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a saƙon ta na Kirsimeti da sabuwar shekara.
Adeyeye ta nuna rashin jin daɗin ta game da yadda magungunan karfin maza su ka cika kasuwannin magani a faɗin ƙasar nan.
A cewar ta, yawancin irin magungunan ma ba su da rijistar NAFDAC ɗin.
“Shigo da su a ke yi ta ɓarauniyar hanya. Inda su na da rijista, to masu shigo da shi da masu sayarwa ba za su riƙa yin abin da su ke yi a kasuwanni, ka tuna, kafafen sadarwa da tituna ba,”
Haka-zalika, wannan kiran na Adeyeye ya zo ne a lokacin da NAFDAC ta ce ta ƙwace jabun magunguna da kayan abinci da darajar su ta kai naira biliyan 3 a filin kasuwar bajakoli a Legas.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp