fidelitybank

NAFDAC ta rufe shagunan magani sama da 11,000 tare da kama mutane 40

Date:

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya Nafdac ta ce ta rufe sama da shaguna 11,000 tare da kama mutum 40 a yaƙin da take yi da sayar da ƙwayoyin jabu.

Da take yi wa ‘yanjarida jawabi a ranar Lahadi, shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce sun tsara samamen ne tun shekara ɗaya da ta wuce.

Zuwa yanzu, Nafdac ta kai samame kasuwanni da dama ciki har da Idumota a Legas, da Ariaria a garin Aba, da Bridge Market a Onitsha a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Ta ce sun hari kasuwanni uku da ke rarraba kashi 80 cikin 100 na magunguna a Najeriya, kuma sun yi nasarar kamawa tare da ƙwace ƙwayoyin jabu da waɗanda ba a yi wa rajista ba.

Farfesar ta kuma sun samu sama da mota 20 ta jabun magunguna a Aba, aƙalla 30 a Onitsha, da wasu 27 a kasuwar Idumota.

“Abin da muka sa a gaba yanzu shi ne fara duba ɗaiɗikun shaguna domin gano masu karya doka da kuma waɗanda ba su da rajista,” in ji ta.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp