Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin “aboki, ɗan’uwa, kuma mai kishin ƙasa”.
“Mai Gaskiya ba tsohon shugaban ƙasa ba ne kawai, mutum ne mai kyawawan ɗabi’u na musamman kuma mai ƙwarin rai a ɓoye, wanda ya ƙaunaci Najeriya hatta a lokacin da aka dinga sukarsa,” a cewar Tinubu cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na zumunta.
Tinubu ya ce yana alhinin mutuwarsa “sosai, ba don kawai ni ne magajinsa ba sai don kasancewarsa tsohon abokin gwagwarmya wajen gina ƙasa”.
A ranar Talata ne Tinubu ya jagoranci jana’izar Buhari a gidansa da ke garin Daura na jihar Katsina. A yau kuma zai jagoranci zaman addu’o’i da na majaliar zartarwa duk domin girmama Buhari.
“Najeriya ta yi rashin ɗa na gari. Ni kuma na yi rashin abokina Shugaba Buhari,” in ji shi.