Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce, ya yi nadamar jagorancin tafiyar da ta bai wa Aminu Tambuwal nasarar zama kakakin majalisa ta bakwai a Najeriya.
Gbajabiamila ya bayyana nadamar tasa ne a lokacin da yake tsokaci kan ‘yan majalisar baya da ya taimaka mawa bayan adawa da zaÉ“in jam’iyya.
Shugaban majalisar ta wakilai, na yin waÉ—annan kalamai ne a wani zaman haÉ—in-gwiwa tsakanin sababbin ‘yan majalisa na APC da kuma sauran jam’iyyun adawa da ke shirin shiga majalisa ta 10 da zaran an Æ™addamar da ita.
Gamayyar ta amince da zaÉ“in da jam’iyyar APC ta yi na Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaba da mataimakinsa a majalisa ta 10.
Har yanzu ana ci gaba da gudanar da wannan zama a Transcorp Hilton, da ke Abuja.