fidelitybank

Na yi mamakin gwamonin dake sukan Buhari – Kwankwaso

Date:

Dan takarar shugabancin Najeriya ƙarkashin jam’iyyar NNPP Injiya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ya yi mamakin yadda ya ga wasu gwamnonin APC ke zagi ko sukar shugaban ƙasar kan sauyin kuɗi.

A wani sako da ɗan takarar ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce bai taɓa tunanin cewa za a kai matakin da wasu daga cikin gwamnonin za su fito su riƙa zagin shugaba Buhari ba.

‘’Haƙiƙa na yi mamakin yadda waɗannan abubuwa suke faruwa, kuma abin sai ya ba ka mamakin me ke damunsu?’’

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce watakila kuma maganar EFCC – cewa wasu daga cikinsu sun ɓoye biliyoyin kuɗi a gidajensu- haka take.

‘’Dan haka wannan tsari da aka zo da shi, zai mayar da biliyoyin kuɗin da suka sace tamkar yayi ko takardu marasa amfani, ina ga wannan shi ne dalilin da ya sa suka fusata’’, in ji Kwankwaso

Ya ƙara da cewa gwamnonin ba suna yi ne don ƙaunar talakawansu ba, domin kuwa a cewarsa babu wani dalili ko hujjar da suka nuna cewa suna ƙaunar talakawan nasu.

Kwankwaso ya kuma ce jam’iyyarsa za ta taimaka wa gwamnatin tarayya musamman a ranar zaɓe wajen sanya idanu domin taimaka wa EFCC da ‘yan sanda da sauran hukumomi wajen fallasa masu amfani da kuɗi domin sayen ƙuri’a.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp