Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya amince cewa yana kewar gasar Premier yayin da ya bayyana sunayen ‘yan wasan da ya fi so.
Da yake magana a Sky Sports News, Wenger ya ce tsofaffin ‘yan wasan Arsenal, Thierry Henry, Dennis Bergkamp, Patrick Vieira, da Robert Pires, sune ‘yan wasan da ya fi so.
Wenger ya ce “Kun rasa ƙarfi da kuma manyan lokutta, masu kyau da mara kyau kuma,” in ji Wenger.
“A zahiri, lokacin da kuka yi aiki na shekaru 22 a ƙwallon ƙafa, hakan yana kama da shekaru 100 a rayuwa ta al’ada. Abin bakin ciki ne, shi ne karshen sha’awa. Har yanzu ina son Arsenal da Premier League. Shine gasar farko da nake kallo har yau. Amma ba ku cikin sa kamar yadda kuka kasance a da kuma hakan yana da wahala. ”
“‘Yan wasan da suka zo a zuciya su ne Thierry Henrys. Haka kuma Dennis Bergkamp tsakanin 2002 zuwa 2004. Vieira da Pires su ma,” Wenger ya kara da cewa, lokacin da aka tambaye shi sunayen ‘yan wasan da ya fi so.
“Bayan haka, kuna da manyan ‘yan wasa, amma ba su sami nasara ba. Wilsheres, Ramsey, Fabregases. Ba za ku iya mantawa da ‘yan wasa ba don haka ba za ku iya zaɓar wanda kuka fi so ba.”


