Gwamnan Jihar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade, ya yi imanin shugaba Buhari ne zai zaba wa APC dan takarar da zai gaje shi.
Ayade ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a ranar Juma’a ya na mai cewa, ya yi imanin Buhari zai zaba wa kasar wanda zai zama alheri.
Ayade ya kuma ce, zai goyi bayan duk wanda jam’iyya ta tsayar ko da Bola Tinubu ne ko Yemi Osinbajo ko kuma waninsu tunda jam’iyya ce ke gaban kowa.
A cewar Ayade, Buhari zai ‘yi abin da ya fi zama alheri ga kasa’ ya shawarci jam’iyyar APC, game da wanda ya kamata a gaje shi, a cewar jaridar The Punch.